1 Peter 3

1Haka ku kuma da kuke matan aure, kuyi biyayya da na ku mazajen, domin in har wadansunsu basa biyayya da maganar Allah, halin matansu ya shawo kansu ba tare da magana ba, 2Domin sun ga tsattsakan halinku da ladabinku.

3Haka ma adonku kar ya zama na kwalliyar waje kitson kai, kayan zinariya ko tufafi masu kawa. 4Amma bari adon ya zama na mutum na cikin zuciya, kuma adon ya zama kyan nan marar dushewa, na kamun kai da natsatsen ruhu, wanda yake da daraja a gaban Allah.

5Haka tsarkakan mata su ka yi ado kamar haka. Suka dogara ga Allah suka yi biyayya ga mazajensu. 6Ta haka Saratu ta yi biyayya ga Ibrahim ta kira shi “ubangiji”. Yanzu ku ‘ya’yantane in dai kun yi aiki nagari, idan kuma ba ku ji tsoron wahala ba.

7Kamar yadda na fada wa matan aure haka ma mazaje, ku zauna da mata da sanin su raunana ne abokan tarayya ne na karbar baiwar rayuwa. Ku dinga yin haka domin a rika jin addu’oinku.

8Daga karshe, dukanku ku hada hankulanku, ku zama masu juyayi, masu kauna kamar ‘yan’uwa, masu taushin zuciya, masu tawali’u. 9Kada ku rama mugunta da mugunta ko zagi da zagi. A maimakon haka ku cigaba da sa albarka, gama sabili da haka ne musamman aka kiraye ku, domin ku gaji albarka.

10“Wanda duk yake so ya more a rayuwarsa ya kuma ga kwanaki masu alheri, to fa, ya kame harshen sa daga mugunta da lebensa daga maganganun yaudara. 11Ya rabu da mugunta ya aikata abin da ke nagari. Bari ya nemi zaman salama ya kuma dimanceta. 12Idanun Ubangiji suna duban adalai, kunnuwansa kuma suna sauraron roke rokensu. Amma fuskar Ubangiji tana gaba da masu aikata mugunta.”

13Wanene ya isa ya cuce ku idan kun himmatu ga yin abin da ke nagari? 14Amma idan kuna shan wuya saboda adalci, ku masu albarka ne. Kada ku ji tsoron abin da su ke tsoro. Kada ku damu.

15Maimakon haka, ku kebe Ubangiji a cikin zukatanku cewa shi mai tsarki ne. Kullum ku zauna da shiri domin ku amsa wa mai tambayar ku dalilin sa begenku ga Allah. Amma fa kuyi haka tare da tawali’u da bangirma. 16Ku zama da tsatsakan lamiri domin mutanen da ke zargin rayuwarku mai kyau cikin Almasihu, su ji kunya domin suna maganar gaba da ku kamar ku mugaye ne. 17Ya fi kyau, a sha wuya akan aiki nagari, idan nufin Allah ne, da a sha wuya sabili da mugun aiki.

18Almasihu ya sha wahala sau daya tak sabili da zunubai. Shi da ya ke mai adalci ya sha wahala domin mu marasa adalci, domin ya kawo mu ga Allah. Aka kashe shi cikin jiki, amma aka rayar da shi cikin Ruhu. 19A Ruhu ne, ya je ya yi wa’azi ga ruhohin da ke a yanzu cikin kurkuku. 20Sun yi rashin biyayya ne sa’adda hakurin Allah yake jiransu a lokacin Nuhu a zamanin sassaka jirgin ruwa, sai Allah ya tsirar da mutane kalilan wato rayuka takwas daga cikin ruwa.

21Wannan kwatancin baftismar da take cetonmu yanzu ne, ba kamar ta wanke Dauda daga jiki ba, sai dai ta rokon Allah da lamiri mai kyau ta wurin tashin Yesu Almasihu daga matattu. Ya hau sama. Yana dama ga Allah. Mala’iku, da mulkoki da masu iko dole su yi masa biyayya.

22

Copyright information for HauULB